Jacob Zuma ya yi tir da kisan baki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Zuma ya yi tir da kashe baki a Afrika ta Kudu

Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya yi tir da hare-haren da ake kai wa baki a kasar, yana mai cewa abu ne da bai dace ba.

A kalla mutane biyar aka kashe tun makon da ya gabata.

Da yake jawabi a gaban majalisar dokokin kasar, Shugaba Zuma ya ce hare-haren da ake kai wa bakin tauye hakkin bil-adama ne da kuma rashin daraja rai.

Dubban mutane ne ke gudunar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Durban na Afrika ta kudu domin bijirewa kin jinin bakin da 'yan kasar ke yi.

Masu zanga-zangar wadanda suka kai 10, 000 na nuna goyon baya ga 'yan kasashen waje da ke zaune a kasar.

A birnin Johannesburg, 'yan kasashen Habasha da Somalia da sauran kasashen Africa sun rufe shagunansu saboda gudun kada a yi musu sata.

Ana zargin fitaccen Basaraken gargajiya na kabilar Zulu da rura wutar kin jinin baki, sai dai ya musanta zargin.

'Yan kasar sun yi zargin cewa baki sun kwace dukkanin ayyukan da suka kamata a ba su, shi ya sa a yanzu kashi 24 cikin 100 na 'yan kasar ba su da aikin yi.wadanda ake zarginsu da karbar ayyukan yi a kasar.

Dubban 'yan kasashen waje -- yawancinsu daga kasashen Africa da nahiyar Asia -- sun yi kaura zuwa Afirca ta kudu tun bayan kawo karshen mulkin fararen fata a shekarar 1994.

A kalla mutane 62 ne suka mutu sanadiyar hare-haren da ke da alaka da kin jinin baki a kasar ta Afrika ta kudu tun daga shekarar 2008.