Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Mutuwar bakin haure a teku

Hakkin mallakar hoto b

A cikin makon nan ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran da a kara daukar matakai wajen ceto rayukan bakin haure dake kokarin ketara teku zuwa kasashen Turai.

Kiran ya zo ne bayan da wasu mutane sama da dari hudu suka mutu a Teku a farkon makon nan.

Yawancin su dai 'yan Afrika ne da kuma wasu 'yan kasashen gabas ta tsakiya da ma Asia.

A makon nan kadai adadin wadanda suka mutu ya aura dari hudu, kuma masu tsaron gabar Tekun Italiya sun ceto mutane sama da dubu goma.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da ke yunkurin tsallakawa zuwa Turai ya yi karuwar da ba'a taba ganin irin ta ba.