Manufar hayaniyar da Orubebe ya yi kenan?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption shugaban hukumar zaben Najeriya Attahiru Jega

A Najeriya, bayanai na ci gaba da fitowa a game da manufar hayaniyar da tsohon Ministan ma'aikatar Naija Delta Godsday Orubebe ya tayar lokacin da ake tattara kuri'u a zaben shugaban kasar na watan Maris da ya gabata.

Wasu wakilan jam'iyyar APC a zauren tattara kuri'un suka ce bayanan da suka samu daga baya, sun nuna cewa manufar hayaniyar da Mista Orubebe ya tayar ita ce a kawo tarnaki ga ci gaba da sanar da sakamakon zaben.

Alhaji Bashir Yusif Ibrahim daya ne daga cikin wakilan jam'iyyar APC a wajen tattara sakamakon zaben, kuma ya ce wasu manya daga yankin Niger Delta sun yi kokarin tada fitina ta yadda za a dakatar da sanar da sakamakon zaben shugaban kasar.

"bayanan da muka samu bayan Orubebe ya yi hayaniya sun tabbatar mana cewa wasu makarraban shugaba Jonathan daga Niger Delta sun yi taro kafin ranar sanar da sakamakon zabe inda suka yanke shawara zasu tada hatsaniya, saboda sun fahimci cewa shugaba Jonathan ba zai yi nasara ba'' in ji Alhaji Bashir.

Ya kara da cewa "cikin abubuwan da suka yanke shawarar yi har da jifan shugabannin INEC da kujeru".

Sai dai Alhaji Bashir ya ce ba shi da masaniya game da rahotannin da ke cewa an yi shirin sace shugaban hukumar zaben Farfesa Attahiru Jega a lokacin da Mista Orubebe ya tayar da hayaniya.

Har ya zuwa wannan lokaci dai bangaren Mista Orubebe bai ce komai game da wannan zargi ba.