An samu raguwar amsa waya ana tuki a England

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Direba yana tuki yana amsa waya

Alkaluman hukumomin 'yan sanda a England da Wales sun nuna cewa an samu raguwar direbobin da ake hukuntawa saboda amfani da wayar salula lokacin da suke tuki da kashi 24 cikin dari a bara.

Alkaluman daga ofisoshi 36 na 'yan sandan sun nuna cewa yawan direbobin da ake kamawa da aikata kananun laifuka ya ragu da fiye da kashi 40 cikin dari daga shekarar 2010 zuwa 2014.

Babban jami'in 'yan sanda dake lura da masu tuka ababen hawa a tituna, Suzette Davenport ya ce jami'ansu suna amfani da dabaru daban daban.

A shekarar da ta gabata, Sakataren fannin sufuri, Patrick McLoughlin ya ce duk direbobin da aka kama suna amfani da wayar salula yayin da suke tuki zasu fuskanci hukunci mai tsanani.

Bayanai sun nuna cewa a shekarar 2013, mutane dubu 95 da 941 ne aka yi wa hukunci mai sassauci bisa amfani da wayar salula lokacin da suke tuki, yayin da a shekarar 2010 aka samu mutane dubu 122 da 752 da irin wannan laifi.