Afirka ta Kudu: An kara kai hare-hare

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hare-hare kan 'yan kasashen waje na ci gaba a South Africa

An kara kai hare hare cikin daren da ya gabata a kan wuraren kasuwanci na 'yan kasashen waje a Afrika ta Kudu.

'Yan sanda sun rika harba hayaki mai sa hawaye da harsasan roba domin tarwatsa gungun masu kai hare haren a gabashin Johannesburg, inda aka cinna wa wata mota da wani gini wuta.

Wani mai magana da yawun 'yan sanda ya sheda wa BBC cewa, kusan 'yan kasashen waje 200 ne suka nemi mafaka a wani caji ofis a cikin daren, amma daga bisani suka tafi.

An dai kara tsaurara matakan tsaro, sakamakon hare-haren da ake kai wa 'yan kasashen wajen musamman 'yan kasashen Afrika, a Afrika ta kudun, inda aka kashe mutane biyar. Shugaban kasar Jacob Zuma ya yi Allah wadai da hare-haren.