Ta'addanci: An kama mutane 5 a Australia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'yan sandan kasar Australia

'Yan sanda a Australia sun ce sun lalata wani yunkuri na kaddamar da harin ta'addanci a wurin da za a gudanar da bukin tunawa da 'yan mazan jiya da suka mutu a yakin duniya na farko.

'Yan sandan suka ce sun kame wasu mutane 5, ciki har da wasu biyu masu shekaru sha takwas-takwas, bisa zargin su da ayukan da suka shafi ta'addanci.

Jami'ai a kasar suka ce mutanen 5 suna shirya yadda zasu kaddamar da hari ne a wurin bukin ranar Anzac a birnin Melbourne cikin makon gobe.

Kimanin jami'an 'yan sanda dari biyu ne aka yi amfani dasu a muhimmin aikin dakile ta'addancin.

A cikin watan Satumban bara ne hukumomin Autralia suka ce kasar tana fuskantar babbar barazana, kuma tun daga wancan lokaci, jami'an tsaro ke kai samame domin kawar da duk wani yunkuri na aikata ta'adanci.