An kashe mutane sama da 20 a kusa da banki a Jalalabad

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Taliban dai na yawan kai hare hare a birnin na Jalalabad

'Yan sanda a birnin Jalalabad na Afganistan sun ce wani harin kunar bakin wake da aka kaddamar ya kashe mutane akalla 22.

Wasu mutane hamsin din kuma sun samu raunuka.

Rahotanni sun ce fashewar ta auku ne kusa da wani banki inda ma'aikatan gwamnati suke karbar albashinsu.

Jami'ai sunce wanda ya kai harin ya zo ne akan babur.

An kuma sami fashewar wani abu na biyu kusa da wani wurin ibada a Jalalabad, amma ba'a kaiga sanin ko harin ya shafi jama'a ba.