'Yan Boko Haram sun kashe kauyawa 10

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Najeriya sun ce 'yan kungiyar Boko Haram sun kashe akalla mutane 10 a kauyen Wala da ke kusa da garin Gwoza a jihar Borno.

Wani dan asalin yankin ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa 'yan Boko Haram sun kashe mutanen ne a wasu hare-haren da suka kai ma kauyen.

Ya ce sun kuma kone gidaje da dama a kauyen.

Lamarin dai ya faru ne a tsakiyar makon nan, amma saboda da rashin hanyoyin sadarwa a yanki ba a samu labarin ba da wuri.

Sojojin Najeriya dai sun kwato garin Gwoza daga hannun 'yan Boko Haram a karshen watan Maris.

Sai dai mazauna yankin sun ce 'yan Boko Haram din da suka tsere suna kai hare-hare a kauyukan da ke kusa da garin.

Karin bayani