Kasashen larabawa su kawo karshen rikicin Libya- Obama

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rikicin Libya na haifar da shigar 'yan cirani nahiyar Turai

Shugaba Obama ya yi kira akan kasashen larabawa da su yi amfani da karfin fada - ajin da suke da shi akan bangarorin Libya masu rikici da juna domin taimakawa wajen warware halinda ake ciki.

Ya ce kasashen Larabawa sun taimaka wajen rura- wutar rikicin kasar Libyar, don haka ya ce yanzu akwai bukatar su taimaka wajen kwantar da kurar rikicin.

Mr Obama ya kara da cewa ba za a iya kawo karshen rikicin ta hanyar amfani da 'yan hare- haren da ake kaiwa da jirage marasa matuka ba- kadai, ko kuma farmakin soji .

Shugaban yana magana ne bayan tattaunawa tare da Firai Ministan Italiya a ziyar da ya kai masa, wanda shi ma ya ce dole ne a dakatar da Yakin basarar Libya, idan har ana son magance kwararar dubban 'yan cirani zuwa nahiyar Turai.