Zuma ya fasa zuwa taron koli a Indonesia

Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma

Zuma ya dage tafiyar ce saboda halin da ake ciki a kasarsa na hare haren da ake kaiwa baki yan kasashen waje.

'Yan sanda a Afirka ta kudu sun bukaci jama'a da su daina akewa da sakonnin da ba'a tantance su ba ta kafofin sada zumunta kan hare haren domin yana haifar da fargaba a zukatan jama'a.

Rundunar 'yan sandan ta ce ta damu matuka da abin da ta baiyana da cewa jita-jitar na rura wutar tarzoma akan baki.

An kama mutane talatin a tarzomar da aka shafe tsawon dare ana yi a Johannesburg.