An sace shanu 400 a Jihar Filato

A Najeriya an sace shanun Fulani makiyaya kimanin 400, kana aka bindige wasu shanun da dama har lahira a karamar hukumar Wase da ke jihar Filato.

Rahotanni sun ce an sace shanun ne lokacin da makiyayan ke wurin kiwo.

Fulanin sun ce barayin sun yi harbe-harbe da manyan bindigogi kafin suyi awon gaba da dabbobin.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti-Allah reshen karamar hukumar ta Wase, Malam Abdullahi Muhammad Yero, ya ce kawowa yanzu ba'a gano shanun ba.

Ya ce tuni sun kai rahoton satar ga hukumomin tsaro.

Matsalar sace-sacen shanu dai na daya daga cikin manyan abubuwa da ke tayar da tarzoma mai nasaba da kabilanci da addini da aka dade ana fuskanta a jihar ta Filato, inda akan samu hasarar rayuka.

Sau da yawa kuma matsalar kan fantsama har zuwa jihar Taraba mai makwabtaka da Filaton.

Tuni dai gwamnan jihar Filaton mai-jiran-gado, Mista Simon Lalong, ya yi alwashin kawo karshen rigingimun, domin ci gaban jihar idan ya kama mulki a karshen wata mai zuwa.

Karin bayani