Sojojin Chadi sun koma Gamborou

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojin Chadi sun sake kafa sansani a Gamborou

Sojojin kasar Chadi wadanda ke zaune a garin Fotokol a Kamaru, sun sake komawa Gamboru a Najeriya inda suka sake kafa wasu sansanoni domin ci gaba da kare rayukan jama'a da kuma fafatawa da kungiyar Boko Haram.

A 'yan kwanakin da suka gabata ne 'yan kungiyar ta Boko Haram suka sake kunno kai a wasu garuruwan karamar Hukumar Kolofata mai iyaka da Najeriya, inda suke kisan rayukan jama'a.

A baya bayan nan wasu mutane kimanin 20 aka raba su da rayukansu.

Ana cewa 'yan Boko Haram din sun sake bullowa ne sanadiyyar yankewar guzurinsu makonni da dama bayan sun lafa kai hare hare musamman ma a Kamaru.