Mutane na fama da karanci abinci a Nijer

Sama da 'yan Nijer miliyan biyu-da-rabi ne ke fuskantar matsalar karancin abinci a bana.

Ministan ayyukan noma na kasar, Malam Maidaji Alambai, ya ce hakan ya biyo bayan rashin kyawon daminar da ta gabata ne.

Ministan ya gaya wa 'yan majalisar dokokin kasar cewa fiye da kashi 15 bisa 100 na jama'ar kasar na fuskantar karancin abinci.

Ya ce rashin isasshen ruwan sama a wasu sassan kasar da kuma ambaliyar ruwa a wani bangaren a daminar da ta wuce sun sanya ba'a samu abinci sosai ba.

Ya ce bincike ya nuna cewa an yi asarar kimanin ton 230,000 na abinci a kasar.

Yawaitar 'yan gudun hijira a kasar kuma zai iya kawo tsananta matsalar.

Nijer na da kimanin 'yan gudun hijira 200,000 a sabili da rikicin Boko Haram a Najeriya da kuma rikicin Mali, kasashe biyu da ke makwabtaka da ita.

Karin bayani