Bakuwar cuta ta halaka mutane 18 a Nigeria

Wata cuta da ba a san irinta ba wacce kuma idan mutum ya kamu da ita ganinsa ke dusashewa sannan yake fita daga hayyacinsa, ta kashe akalla mutane 18 a kudu maso yammacin Nigeria

Jami'an lafiya a jihar Ondo sun ce gwaje- gwajen da aka yi bai nuna cewa kwayar cutar ebola ce ke haddasa ta ba.

Magidanta sun ce cutar ta soma barkewa ne kwanaki hudun da suka gabata, kuma ta na bazuwa sosai, inda take hallaka wadanda suka kamu da ita cikin sa'oi 24.

Kwamishinan lafiya na jihar Ondo ya ce hukumomin Nigeria na aiki tare da kwararru daga kungiyar lafiya ta duniya WHO ,domin gano kowacce irin cuta ce

Babban jami'in gwamnatin ya shawarci jama'a dasu daina taba gawar wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.