'Maganin kwari ne ya kashe mutane a Ondo'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce maiyiyuwa maganin kashe kwari, ko kuma na kashe ciyawa, shine musababbin cutar nan da ba'a san kanta ba a Najeriya.

Cutar dai ta yi sanadiyar mutuwar mutane 18 a kudu maso yammacin Najeriyar.

A 'yan kwanakin nan wasu mutane a jihar Ondo sun mutu 'yan sa'o'i kadan bayan kamuwa da ciwon kai da kuma dusashewar gani.

Kakakin Hukumar Lafiya ta Duniyar, Gregory Hartl, ya ce gwajin da aka yi kawo yanzu bai nuna alamar kwayar cutar virus ko kuma bacteria ba.

Ya ce hasashen da suke da shi a yanzu shine cewa maganin kashe kwari, ko na kashe ciyawa, shine ya haddasa mutuwar mutanen.

A ranar Asabar dai jami'an lafiya a jihar Ondon sun ce gwaje-gwajen da aka yi bai nuna cewa kwayar cutar Ebola ce ke haddasa cutar ba.

Magidanta sun ce cutar ta soma barkewa ne a makon da ya gabata, kuma ta na bazuwa sosai, inda ta ke halaka wadanda suka kamu da ita cikin sa'o'i 24.

Kwamishinan lafiya na jihar ta Ondo ya ce hukumomin Najeriya na aiki tare da kwararru daga Hukumar Lafiya ta Duniyar domin gano kowace irin cuta ce.

Babban jami'in gwamnatin ya shawarci jama'a dasu daina taba gawar wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.

Karin bayani