Boko Haram: Yara 800,000 ne su ka yi hijira

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rikicin Boko Haram ya tarwatsa yara da dama zuwa wasu kasashen

Kimanin yara dubu dari takwas ne aka tilasta musu yin gudun hijira zuwa kasashen Kamaru da Chadi, sakamakon hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram su ke kai wa a Nigeria.

Rahoton da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya wallafa game da wannan lamari, ya zo ne shekara guda bayan sace 'yan matan Chibok da aka yi a garin Chibok na jihar Borno.

Rahoton kuma ya ci gaba da cewa an tilasa wa karin wasu yaran zama sojojin haya, a yayin da kuma ake cin zarafin tarin wasu 'yan mata.

A kan haka ne UNICEF din tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi da kuma hukumomi suka fara ba da tallafi ga wasu dimbin yaran da aka samesu a kebe.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane kusan 15,000 a cikin shekaru biyar a Nigeria.