Tarayyar Turai na taro kan mutuwar 'yan ci rani

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministocin harkokin wajen kasashen Tarayyar Turai

A yau ne Ministocin harkokin wajen kasashen Tarayyar Turai suke taro a Luxembourg domin tattauna mutuwar 'yan ci rani da ke ketara tekun Meditareniyan daga Afirka.

A bara ne Tarayyar Turan ta yanke shawarar takaita aikin ceton mutane a tekun a matsayin dabarar hana 'yan ci rani ketara tekun.

Sai dai wasu kasashen kudancin Turai sun ce kadarin Tarayyar zai iya faduwa, muddin bata sake nazarin shawarar data yanke ba.

A ranar Lahadi wani kwalekwalen dauke da 'yan ci rani kimanin 650 ya kife a tekun Mediterranean.

Kwalekwalen ya kife ne lokacin da fasinjojin suka tattaru a gefe daya inda suke kokarin shiga wani babban jirgin ruwa dake kusanto su.

Kasar Italiya ta shirya aikin ceto da za a yi amfani da jiragen ruwa 20 da jirage masu saukar ungulu 3.