Daliban Jami'a na yajin shiga aji a Nijar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dalibai na yajin karatu a Nijar domin matsa wa gwamnati lamba ta inganta harkar ilmi

A ranar Litinin ne daukacin daliban jami'o'i hudu a Jamhuriyar Nijar su ka soma wani yajin shiga aji na kwanaki biyu domin ci gaba da matsa wa gwamnati lamba har sai ta dauki matakan kyautata wa daliban yanayin karatunsu da na rayuwa.

Abdulkadir Abu-kwaini shi ne shugaban kungiyar daliban jami'ar Yamai kuma kakakin kungiyoyin daliban kasar ya shaida wa BBC cewa bukatunsu masu ma'ana ne.

"Muna fama da rashin Malamai, tsirarun malaman da ake dasu su ke koyarwa a dukkan jami'o'in kasar, hakan ya na jawo rashin fitar da sakamakon jarrabawa cikin lokaci."

Sai dai ministan ma'aikatar ilimi mai zurfi na kasar Malam Usman Abdu, ya ce ya na tattauna wa da kungiyoyin daliban jami'o'in domin warware matsalolin.

"Rashin hakuri ne ya kawo hakan, amma ai dama tuni gwamnati ta fara shirye-shiryen yi wa harkar ilimi garanbawul kuma nan ba da jimawa ba komai zai dai-daita," in ji Malam Usman.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne dai kungiyoyin daliban jami''o'in Yamai da Maradi da Damagaram da Tawa suka yi wani taro a kan neman hanyar warware matsalolin da su ka yi wa jami'o'in kasar dabaibayi, in da suka bai wa gwamnati wa'adin kwanaki bakwai domin warware matsalolin ko kuma su kauracewa ajujuwa.