APC ta musanta rarraba mukaman siyasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Nigeria mai jiran gado

Jam'iyyar APC ta bukaci 'yan Nigeria su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewar ta rarraba mukamai zuwa shiyyoyin siyasar kasar a gwamnatin Janar Buhari mai kamawa.

Sanarwar da kakakinta, Lai Mohammed ya fitar, ta ce "babu kanshin gaskiya a kan cewa an raba wasu mukaman shugabanci zuwa wasu shiyoyin kasar."

Matakin jam'iyyar APC na zuwa ne bayan da wasu jaridun Nigeria suka wallafa cewa an cimma wani tsarin rabon mukaman siyasa a kasar musamman na shugabannin majalisar datijjai da ta wakilai, da kuma yadda za a raba mukaman ministoci a fadin kasar.

Tun bayan da Janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasa, 'yan siyasa suka soma kamun kafa a kan yadda za a raba mukamai a tsakanin shiyyoyin siyasa a kasar.

Wasu shiyyoyin kasar dai tuni suka fara fafutukar a ba su shugabancin majalisar dattijai ko ta wakilai, yayin da wasu 'yan majalisa suka fito da bukatarsu fili, ta neman shugabancin majalisun.