Ma'aikatan INEC sun yi zanga-zanga a Bauchi

Image caption A ranar 28 ga watan Maris da 11 ga watan Afrilu ne aka gudanar da zabuka a Nigeria

A jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Nigeria wasu matasa sun yi zanga-zanga a babban birnin jihar game da zargin rashin biyansu hakkokinsu da hukumar zaben kasa INEC ta ki yi.

Ma'aikatan dai na zargin cewa duk da wahalar da suka ce sun sha a yayin gudanar da zaben, hukumar ta INEC reshen jihar Bauchi ba ta mayar da hankali wajen biyansu kudaden alawus na aikin zabe ba.

Duk da cewa hukumar zaben ta fara wani yunkuri na biyansu kudaden, ma'aikatan sun kuma yi zargin cewa ana zaftare wani adadi daga cikin kudin.

Daya daga cikin masu zanga-zangar Sani Muhammad Datti ya shaida wa BBC cewa hukumar zaben ta nemi sulhu bayan da dimbin matasan suka tare hanyoyi a ranar Litinin, "Amma sulhun nasu bai yi amfani ba duk da cewa sun fara biyan kudaden amma sai suke yanke naira 8,000 daga cikin kudin."

A nata bangaren hukumar zaben ta ce tana kokarin biyan masu zanga-zangar hakkokinsu.

Shugaban hukumar zaben jihar Alhaji Aliyu Abubakar, yace "tun da fari 'yan bautar kasa ne ya kamata su yi aikin shi yasa muka tura kudin hukumar bautar kasa amma yanzu mun nemi su dawo da kudin domin biyan wadannan matasa."