Jonathan ya cire Shugaban 'yan sandan Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Tsohon sufeto janar, Sulaiman Abba

Shugaban Nigeria mai barin gado, Goodluck Jonathan ya cire Sulaiman Abba daga mukamin sufeto janar na 'yan sandan kasar.

Kakakin Mr Jonathan, Rueben Abati ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa an nada DIG Solomon Arase a matsayin sufeto janar na riko.

Fadar shugaban kasar ba ta bayyana dalilan da suka sa aka cire Sulaiman Abba daga mukamin ba.

Sai dai ana zargin 'yan sandan kasar da tsoma baki a harkokin siyasa, zargin da suka musanta.

A cikin watan Yulin 2014 ne Mr Jonathan ya nada Sulaiman Abba a matsayin babban sufeto janar na 'yan sanda bayan da Mohammed Abubakar ya yi ritaya.