Shugaba Mahama ya ziyarci Jonathan da Buhari

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Nigeria na taka muhimiyar rawa a kungiyar ECOWAS

Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya kai ziyara ga shugaban Nigeria mai barin-gado, Dr Goodluck Jonathan a fadarsa da ke Abuja.

Mr Mahama wanda ya kai ziyarar a matsayinsa na shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma watau Ecowas, ya ce manufar ziyarar ita ce domin taya Nigeria murnar gudanar da zabe cikin lumana a watan da ya gabata.

Sun shafe kusan awa guda suna tattaunawa a cikin sirri tsakaninsu a cikin fadarta Aso Villa da ke Abuja.

Haka kuma shugaban na Ghana, ya tattauna da shugaban kasar mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari.

Sannan ya kuma gana da shugaban hukumar zabe ta Nigeria INEC, Farfesa Attahiru Jega.