Tsohuwa 'yar shekaru 65 za ta haifi 'yan hudu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Annegret Raunigk, a lokacin ta na da shekaru 55, tare da 'yar autarta, Leila

A kasar Jamus, an samu wata malamar makaranta mai shekara 65 dauke da cikin 'yan hudu.

Wannan tsohuwa mai suna Annegret Raunigk tana cikin koshin lafya, kuma in har abubuwa sun tafi yadda ya kamata, za ta zama ta farko da za ta haifi 'yan hudu a shekarun ta, amma ba ita ce ta farko da za ta haihu da tsuffa ba.

A kasar Spaniya a 2006, an samu Maria del Carmen Bousada Lara da ta haifi 'yan biyu tana shekara 66, da kuma Omkari Panwar wacce a shekara 70 ta haifi 'yan biyu a India.

Ta yaya tsofaffi ke samun juna biyu?

Gudunmuwar kyau

Duk matan da suka daina haila ba za su iya daukar ciki ba sai da taimakon likita.

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Kwan da ke jikin mata

Suna bukatar wasu matan da za su ba su gudunmuwar kyau domin a dasa a cikinsu.

Jarirai mata ana haihuwar su da dukkan kwayayensu, kuma da zarar sun soma haila, kwayayen suke fara raguwa, amma da zarar sun shige shekara 40, kwayayen sai su rage karfi.

Saboda haka mata da suka wuce shekarun haihuwa sai an taimaka masu su kafin su samu juna biyu.

Kyayoyin halitta

Likitoci suna baiwa irin wadannan mata wani sinadari mai suna Oestrogen, saboda mahaifar ta shirya karban kwai.

A yayinda shi kuma kwan da za a ba ta gudumuwar sa ne ko kuma in nata na da sauran armashi yana adane a daskare--- sai a sa mata a mahaifar ta.

Dr. Sue Avery, kwararriyar likitar mata ce a asibitin Birmingham, ta ce " Aikin dai ba shi da bambanci da yadda muke yi wa 'yan mata, duk da cewa su 'yan mata sai har an cire masu mahaifar su tukunna".

Likitar ta yi kara da bayanin cewa ya kamata tsofaffi masu juna biyu su yi kokarin kulawa da jikinsu, saboda su za su fi saurin kamuwa da hawan jini, ciwon suga da makamantan su.

Gudumuwar kwan budurwa ya fi armashi, kuma tsohuwar ta fi samun lafiyar cikin.

Hakkin mallakar hoto Getty

A wani bincike da Amurka ta yi, an gano cewa wahalhalun da tsohuwa mai juna biyu take shiga da kuma na budurwa duk kusan daya ne, in dai har gudumuwar kwan da suka samu duk ta hanya daya ce.

Tiyata

Matsalar da Ms Raunigk za ta fuskanta shi ne 'yan hudu ne ta ke dauke da su.

Dr. Avery ta ce, haihuwar 'yan biyu, ko 'yan uku, ko 'yan hudu, suna zuwa da matsaloli daban-daban, kamar hawan jini, da kumburin kafa, kuma da wuya ta iya haihuwa da kanta saboda dole ne ayi mata aiki.

Wannan tsohuwa mai shekara 65, tana da 'ya 'ya 13, kuma ta haifi 'yar autan ta shekara 10 da suka wuce.

Likitan ta Dr. Kai Hertwig ya yi bayanin cewa haihuwar 'yan hudu na da wuya, amma a yanzu matar tana cikin koshin lafiya.