Za a tallafa wa 'yan gudun hijira a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan gudun hijira ne suke fama da rashin kayayyakin more rayuwa.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR ta kaddamar da wani shiri a Kamaru domin tallafawa 'yan gudun hijira su samu ayyukan yi da kuma zama masu dogaro da kai.

Shirin dai ya hada da koyar da 'yan gudun hijirar sana'o'in hannu kamar dinki da noma da kuma kasuwanci.

A yanzu haka an fara share fagen wannan shiri a garin Pitoa da ke arewacin kasar, inda aka zabi iyalai 20 da ake gwaji da su.

Za a kuma ci gaba da yada shirin akan sauran 'yan gudun hijira da ke kasar.

Dubban 'yan gudun hijirar Nigeria da Jamhuriyar Nijar ta tsakiya ne suke samun mafaka a Kamaru sakamakon hare-haren da 'yan Boko Haram ke kai wa a kasashensu.