Habasha: An yi zanga-zanga kan kisan da IS ta yi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Habasha ta tabbatar da cewa 'yan kasar ta ne kungiyar IS ta kashe bidiyo.

Dubban mutane suka halarci wata zanga-zangar da aka yi a Addis Ababa, babban birnin Habasha domin jimamin kashe 'yan kasar da kungiyar IS ta yi a Libiya.

Tarzoma ta barke tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar, inda masu zanga-zangar ke cewa gwamnatin kasar ba ta dauki mataki a kan kisan ba.

Wani bidiyo da kungiyar IS ta sanya a shafin intanet a karshen makon jiya ya nuna yadda aka kashe mutanen, inda aka fille kawunansu, kuma aka harbe su.

Gwamnatin Habasha ta tabbatar cewa mutanen da aka kashe a bidiyon 'yan kasar ne.