Matar da ta kirkiri tutar Ghana ta mutu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mrs Theodosia ce ta zayyana tutar Ghana a shekarar 1957.

Shugaban Ghana, John Mahama, ya bayar da umarnin a sassauto da tutocin kasar a dukkan gine gine har na tsawon kwanaki uku don karrama marigayiya Mrs Theodosia Okoh, matar da ta zayyana tutar kasar.

Mrs Okoh ta zayyana tutar Ghana ne a shekarar 1957 lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Biritania.

Mrs Theodosia Okoh dai ta rasu ne a ranar Lahadi da ta wuce tana da shekaru 92 da haihuwa a wani asibiti da ke birnin Tema kusa a birnin Accra.

Marigayiyar ta yi fice wajen son kwallon doki, kuma ita ce mace ta farko da ta zama shugabar kungiyar kwallon doki ta Ghana.