Sankarau: Za a rufe makarantu a Niger

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Mutane tamanin ne suka mutu a Nijar sanadiyar kamuwa da sankarau a shekarar 2015.

Rahotanni daga jamhuriyar Niger na cewa za a rufe dukkannin makarantun kasar na wasu kwanaki a wani yunkuri na dakile cutar sankarau a fadin kasar.

Kididdiga ta nuna cewa cutar ta sankarau ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 80 a shekarar 2015.

Firai ministan kasar, Bragini Rafini, ya kaddamar da wani shiri na allurar rigakafin cutar sankarau ga yara masu shekaru 2 zuwa 15.

Sai dai Firai Ministan ya yi kira ga kungiyar lafiya ta duniya da ta agaza wa kasar domin samar wadatacciyar allurar rigakafin.