Sankarau: An rufe makarantu a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane kusan dari tara ne suka kamu da cutar ta sankarau.

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun rufe makaruntu a Yamai, babban birnin kasar a wani yunkuri na dakile barkewar cutar sankarau da ta kashe mutane fiye da 80 a shekarar da mu ke ciki.

Firai ministan kasar, Brigi Rafini, ya kaddamar da shirin allurar rigakafi ga dukkanin yara masu shekaru 2 zuwa 15, sai dai ya ce Nijar tana da rabin alluran rigakafin da ake bukata.

Sai dai Firai Ministan ya yi kira ga kungiyar lafiya ta duniya da ta agaza wa kasar domin samar wadatacciyar allurar rigakafin.

Mutane kusan dari tara ne suka kamu da cutar.