Ba zan je kowacce kasa ba — Diezani

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana min kazafi ne saboda na takura wa wasu kuraye inji Mrs Diezani Allison Madueke

Ministar albarkatun mai ta Nigeria, ta ce ba ta da niyyar ficewa daga kasar duk da almundahanar biliyoyin dala da ake zarginta da tafkawa.

Mrs Diezani Allison Madueke na mayar da martani ne ga labarin da ake bazawa a shafukan intanet cewa ta nemi mafakar siyasa a kasashe shida bayan kayen da Jam'iyyar PDP ta sha a zaben kasar.

Ta ce "Ba wani laifi da ta aikata da za ta nemi mafaka a wata kasa, tana mai musanta zargin kudaden da aka ce ta kashe kamar naira biliyan goma wajen yawo a jirgin sama."

Ministar ta ce ya kamata a daina masu irin wannan kazafi ta shafukan intanet da ta ce wasu matsorata na yi, domin a cewarta ta yi wa Najeriya aiki iya iyawarta a ma'aikatar ta mai.

Kazalika ministar ta musanta cewa ta je gidan tsohon shugaban kasar Abdussalami Abubakar domin rokonsa ya nema mata sassauci wajen shugaban kasar mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari.