PDP ta yi wa tsofaffin 'ya'yanta raddi

Hakkin mallakar hoto muazu facebook
Image caption Shugabannin PDP sun ce za su dukufa don dawowa mulki a 2019

Jam'iyyar PDP mai mulki a Nigeria, ta ce masu turuwar barin jam'iyyar suna komawa APC mai jiran gado ba 'ya'yanta ba ne na ainahi, 'yan halak.

A wata hira da BBC ta yi da mataimakin shugaban jam'iyyar ta PDP, Ambassada Ibrahim Kazaure, ya ce, dukkanin masu sauya sheka daga jam'iyyar bayan da ta fadi a zaben kasar daman ba 'yan halaliyarta ba ne.

Mataimakin shugaban na PDP, yana wadannan kalamai ne bayan wani taron shugabannin jam'iyyar ya sha alwashin ci gaba da ganin jam'iyyar ta farfado daga koma bayan da ta samu a zaben da ya gabata.

Taron ya ce zai ci gaba da mara baya ga shugabancin jam'iyyar karkashin jagorancin, Alhaji Ahmad Adamu Mu'azu, domin sake komawa kan karagar mulki a 2019.