Sojojin Nigeria sun kai hari a dajin Sambisa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Najeroya sun kai hari dajin Sambisa.

Sojojin Najeriya sun ce suna kai hare-hare a dajin Sambisa, wurin da ake gani shi ne maboya ta karshe da kungiyar Boko Haram ke zama.

Kakakin rundunar sojin, Chris Olukolade, ya tabbatar da cewa sojin suna kai farmaki a dajin Sambisa, wanda ke kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Gwamnatin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram sun gudu, kuma ta sha alwashin dakile hare-haren da suke kai wa kafin rantsar da Shugaba mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari, ranar 29 ga watan Mayu.

Ana zaton 'yan matan Chibok sama da 200 da kungiyar ta sace, suna rike da su ne a dajin Sambisa.