Rikici ya barke a Sudan ta Kudu

Image caption An sha fafatawa tsakanin sojin gwamnati da na sa-kai a Sudan ta Kudu.

Fadar ya barke tsakanin sojoji da kuma sojin sa-kai da ke goyon bayan gwamnati a birnin Malakal da ke da arzikin man fetur na kasar Sudan ta Kudu.

Bangarorin biyu sun fara fafatawa ne a daren ranar Talata a gidan gwamnan jihar.

Mutane da dama sun ji rauni, kuma kimanin mutane dubu biyu ne suka nemi mafaka a sansanin Majalisar Dinkin Duniya da ke yankin.

Birnin na Malakal, wanda ke arewa maso gabashin jihar Upper Nile, ya sha fama da fadace-fadace tun lokacin da yakin basasa ya barke a Sudan ta Kudu a watan Disamba na shekarar 2013, kuma a lokuta da dama ya sha sauya hannu daga wajen sojin gwamnati da na sojin sa-kai.