Yemen: Saudiyya ta ce tayi nasara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun sojin hadin gwiwa da kasar Saudiyya take jagoranta a Yemen

Kasar Saudiyya ta ce tayi nasarar dakile barazanar da 'yan tawayen Houthi mabiya mazahabar shi'a ke yi wa kasar Saudiyya daga Yemen.

Saboda haka kasar ta amince da zama da 'yan tawayen domin yin sulhu.

Sai dai kuma wasu na ganin cewa Saudiyyar ta gano 'yan Houthin za su gagare ta ne, shi yasa ma ta amince da yin sulhun.

Saudiyya dai ta kasance kasa da tafi kowacce kusanci da Yemen.

A watan Janairun 2015 ne dai 'yan tawayen Houthi suka afka wa babban birnin kasar Yemen, Sana'a, a inda suka tilastawa shugaban kasar, Abd-Rab Mansour Hadi ficewa daga birnin.