Fada ya sake rincabewa a Yemen

Hakkin mallakar hoto
Image caption Fada ya sake rincabewa a Yemen

Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a hedikwatar sojoji da ke karkashin ikon mayakan sa-kai mabiya Shi'a na Houthi a garin Taez da ke Yemen, sa'o'i kadan bayan da rundunar soji da Saudiyya ke jagoranta ta dakatar da kai hare-hare a kansu.

Tun da fari dai Iran ta bayyana matakin da Saudiyya ta dauka na dakatar da kai hare-haren a matsayin kyakkyawan ci gaba, ta kuma yi kira da a kawo karshen fadan.

Wakilin BBC a gabas ta tsakiya da ke Jidddah ya ce duk da cewa Saudiyya ta ce ita ta yi nasara a matakin farko na kamfe dinta, har yanzu ba a karbo ikon gwamnatin Yemen ba.

A cewarsa, har yanzu 'yan tawayen ne ke rike da ikon babban birnin kasar, Sana'a.