Indonesia za ta kashe masu safarar kwayoyi

Hakkin mallakar hoto JEWEL SAMADSONNY TUMBELAKASTRBAY ISMOYOMETRO TVSURYO WIBOWOAFPGetty Images
Image caption Indonesia ta yi watsi da kiraye kirayen neman ka da ta kashe mutanen

Hukumomin Indonesia sun gayyaci jami'an ofisoshin jakadanci na kasashen waje zuwa wani kurkuku mai tsananin tsaro inda za a aiwatar da hukuncin kisa a kan wasu masu safarar miyagun kwayoyi su goma yawancinsu 'yan kasahen waje.

Duk da cewa ba a bayar da sanarwar aiwatar da hukuncin kisan wadda a hukumance aka saba bayarwa ba sa'o'i 72 kafin hukuncin, wani jami'in diflomasiyya ya ce yana ganin za a aiwatar da hukuncin kisan cikin 'yan kwanaki.

Masu safarar miyagun kwayoyin da za a kashe ta hanyar bindigewa sun hada da 'yan kasashen Najeriya da Faransa da Brazil da Phillipines da kuma Australia.

Faransa da Brazil da Australia sun gargadi Indonesian da cewa muddin ta aiwatar da hukuncin kisan to za ta ga abin da zai biyo baya da ba zai mata dadi ba.

Sai dai kuma duk da kashedin hukumomin na Indonesia sun kafe cewa sai sun aiwatar da hukuncin.