An yi jana'izar 'yan ci-rani 24 a Malta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har yanzu ba a gawawwakin mutane da dama

An yi jana'izar mutane 24 daga cikin 'yan ci-ranin da suka nutse a cikin tekun Bahrum a ranar Asabar din da ta gabata.

Su ne kadai gawawwakin da tawagogin masu aikin ceto suka gano daga kwale-kwalen kamun kifin da aka bayyana ke dauke da mutane 800 daga kasar Libya zuwa Turai.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana hadarin da mafi muni da ya taba abkuwa ga 'yan ci-ranin.

A waje daya kuma shugabannin Tarayyar Turai na can a birnin Brussels suna tattaunawa kan shawarar da kasar Italiya ta gabatar, na daukar matakan soja a kan masu safarar irin wadannan bakin haure daga kasar Libya.

Hukumomin Italiyar na son ganin ana lalata irin wadannan jiragen ruwa na masu fasa-kwaurin, tun ma kafin su bar tashoshin da suka tashi daga cikinsu.