An yi jana'izar 'yan ci-rani

Image caption Daya daga cikin akwatin gawawwakin fari mai lamba 24 gawar wani yaro ne a ciki.

An yi jana'izar 24 daga cikin 'yan ci-ranin da suka nutse a tekun Bahar Rum a ranar Asabar din da ta gabata.

Gawawwakin dai su ne kadai wadanda tawagogin masu aikin ceto suka gano daga kwale-kwalen kamun kifin da aka ce yana dauke da mutane 800 daga kasar Libya zuwa Turai.

Wasu daga cikin 'yan ci-ranin da suka yi irin wannan tafiya ta tekun Bahar Rum su ma sun bi sahun jami'an gwamnatin Malta wajen jimamin rashin da aka yi.

Mata daga kasashen Somalia da Eritrea da kuma wasu daga kasashen da ke yankin kudu da sahara sun barke da kuka yayin da aka jere akwatunan gawar akan jan karpet.

Sojoji sun yi ta bushe-bushen algaita a kan gawawwakin, kuma an gabatar da addu'o'i na Musulmai da Kirista a karkashin jagorancin Imam Mohammed El Sadi da Bishop na Gozo Monsignor Mario Grech, inda suka karanto addu'o'i daga Al-kur'ani da Bible.

Imam Sadi ya kuma ce "Wannan abu daya faru ya tuna mini cewa mu ma fa duk baki ne kuma anan duniya matafiya ne."

Duk da kasancewar ba a san iyalan wadanda suka mutun ba, za a binne sune a makabartar Addolorata da ke Malta.

A hannu guda kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya kamata kasashen Turai su yi alkawarin zasu kara yawan yan gudun hijira da suke karba a kasashensu da kuma samar da halattattun hanyoyin kaura ba tare da hadari ba.