An kashe ma'aikatan agaji a wani harin sama

Warren Weinstein Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ma'aikacin agaji Dan Amurka da aka kashe

Fadar white house ta ce an kashe wasu 'yan kasashen yamma da ake garkuwa da su,a harin da wani jirgin sama marar matuki na Amurka ya kai a kan iyakar Afghanistan da Pakistan, a watan janairun da ya gabata.

Shugaba Obama ya ce bai ji dadin cewar an kashe ma'aikatan agaji, Ba-Amurke da Giovani Lo Porto dan kasar Italiya, bisa kuskure ba.

Kungiyar Al-Qaeda ta dade tana garkuwa da mutanen biyu.

Sai dai shugaba Obama ya ce Amurka ba ta san cewa ana tsare da su a gidan da aka kai wa hari ba.