"Za mu kai Sarkin Zulu kotun ICC" - Serap

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a kai sarkin Zulu kotun ICC

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta SERAP da ke Nigeria ta bukaci a gurfanar da sarkin Zulu a gaban kotun duniya ta hukunta manyan laifuka bisa kalaman da ya yi wadanda suka hura wutar rikicin da 'yan kasar suka kai hare-hare kan baki.

Kungiyar ta SERAP ta bayyana bukatar hakan ne a wata sanarwa da shugabanta Adetokunbo Mumuni ya sanya wa hannu.

Kungiyar ta kuma yi kira ga babbar mai shigar da kara ta kotun ICC Fatou Bensouda da ta tabbatar ta yi bincike sosai tare da hukunta sarki Goodwill Zwelithini, saboda rigimar wacce ta jawo aka kashe rayuka bakwai na 'yan Afrika da kuma tabbatar da dokar da za ta hana afkuwar irin wannan a gaba.

SERAP ta kuma bayyana al'amarin na Afrika ta kudu da cewa cin zarafi ne tare da keta hakkin bil'adama.

Ana dai zargin sarki Goodwill Zweletheni da hura wutar rikicin ne bayan da ya bukaci baki da su fice daga Afirka ta Kudun.

Amma sarkin ya musanta hakan.