Ana gangami kan kin jinin baki a Afrika ta Kudu

Image caption Zanga-zangar adawa da kin jinin baki a Afrika ta kudu

Dubban 'yan kasar Afrika ta Kudu sun soma gudanar da gangamin nuna rashin amincewa da tashin hankalin da ya faru a baya-baya nan mai nasaba da kyamar baki.

Ana gudanar da gangamin ne a Johannesburg da kuma garin Port Elizabeth mai tashar ruwa, inda aka kai wa baki hare-hare a shekarar 2008.

Marc Gbaffou jami'i ne a daya daga cikin kungiyiyon da suka shirya gangamin, ya ce "muna son mu isar da sako mai karfi ga sauran al'ummar kasar Afrika ta kudu da kasashen Afrika da kuma duniya baki daya a kan cewa wasu tsirarun mutane ne a kasar Afrika ta kudu, su ke kokarin shafa kashin kaji ga kasar."

Jami'an tsaro sun kai sameme a wasu wurare a garin Alexandra da ke Johannesburg, inda aka fi kai wa baki hare-hare a 'yan makwannin da suka gabata.

A jihar Kaduna da ke Najeriya ma wasu matasa ne suka yi zanga-zanga a babban ofishin kamfanin sadarwa na MTN mallakin 'yan kasar Afirka ta Kudu, domin dakatar da ayyukan kamfanin na yau da kullum, da zummar nuna adawa da cin zarafin da ake yi wa baki a Afrika ta kudun.