Google ya fara sana'ar wayar hannu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Google zai fara sana'ar wayar hannu

kamfanin Google ya bayyana tsarinsa na tafiyar da harkar wayar hannu a Amurka.

Bisa tsarin, kamfanin zai rinka yin amfani da tsarin intanet daga kamfanonin Sprint da na T-Mobile.

A karon farko, masu amfani da wayar hannu samfirin Nexus 6 ne za su ci gajiyar tsarin.

Wannan tsari da Google zai amfani da shi yana da karfin gaske kuma zai ba wa abokan huldatayyarsa samun tsarin intanet mai matukar sauri.

Sai dai kuma kamfanin ba shi da cikakken iko kan tsarin saboda ya dogara ne da wasu kamfanonin.

Hakan yasa wasu kwararru ke ganin cewa yin amfani da kayan aikin wasu kamfanoni wadanda abokan hamayyarsa ne ke samar masa da tsarin.

Ana ganin dai cewa za a iya yi wa kamfanin makarkashiya.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption a baya baya ma kamfanin ya fito da komputa samfirin memory card

Wasu ma na ganin cewa kamfanin ba zai iya tafiyar da harkar ba.