An gargadi Biritaniya kan 'yan ci-rani

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad al Hussein

Babban jami'in hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra'ad al Hussein ya bukaci gwamnatin Biritaniya da ta magance abin da ya kira kalaman da ke zuzuta kiyayyar 'yan ci-rani da kafafen yada labaran kasar ke yi.

Ya ambaci wata makala da jaridar Sun ta buga a baya-bayan nan, inda ta danganta 'yan ci-ranin Afrika da kyankyasai, yana mai cewa irin wannan kalmar ce kafafen yada labaran Rwanda suka yi amfani da ita gabannin kisan kare dangin da ya faru a kasar.

Mr Hussein ya yi gargadi cewar Biritaniya ba ta kalubalantar irin wadannan munanan kalamai a kan 'yan gudun hijira da masu neman mafaka, wanda hakan ka iya zama illa ga kasar.

Ya kuma ce tilas hukumomin Biritaniya su tuna cewa suna amfani da dokar duniya da ta kasarsu wadanda suka haramta amfani da kalaman tunzura kiyayya.

Wakilin BBC a Geneva yace jawabin ya daga hankalin Majalisar Dinkin Duniya ganin cewa irin wadannan kalamai da kafafaen yada labarai ke yi na iya kawar da hankalin jama'a daga son taimakawa a yunkurin daukar mataki domin ceto rayukan 'yan ci rani a tekun Bahar Rum.