Ana son dakatar da China daga kirkirar dan tayi

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Masu bincike a China na kokarin kirkirar dan tayin dan adam

Masana kimiyya na duniya sun yi kira da a dakatar da masu bincike 'yan kasar China daga yunkurin da suke yi na kirkirar kwayoyin halittar dan tayin dan adam.

An yi amanna wannan shi ne karo na farko a duniya da masana kimiyya a jami'ar Guangzhou suka yi amfani da dabarar gwajin kwayoyin halitta domin yanka kwayoyin halittar da ke da alaka da matsalar cutar jini, sannan suka maye gurbin ta da kwayoyin halittar dan tayi mai lafiya guda 86.

Binciken -- wanda babbar mujallar "Science and Nature on ethical ground", ta ki amince wa da shi -- ya sha Allah-wa-dai a wajen manyan masana kimiyya na duniya, inda suke kallonsa a matsayin wani yunkuri na samar da jariran gaibu.