New Zealand ta zargi Turkiyya da kisan kiyashi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Firaiministan New Zealand, John Key

Firaiministan, New Zealand, John Key ya zargi kasar Turkiyya da laifin kisan kiyashi akan sojojin kasar shekaru dari da suka gabata.

John Key ya yi wannan zargin ne a ranar Asabar yayin taron dubban mutane daga kasashen Australia da New Zealand a birnin Gallipoli na kasar Turkiyya domin tunawa da kisan kiyashi sojojin kasashen biyu har dubu 11 da dari hudu, a kasar ta Turkiyya, a shekarar 1915.

John Key cewa yayi "bakon abu ne ayi wa kasarsa kallon barazana ga wata kasa, amma irin wannan kallo daular Ottoman ta Turkiyya tayi wa kasar tasa shekaru dari da suka gabata".

Shi ma firaiministan Australia, Tony Abott ya shaidawa gangamin cewa dakarun Australia wadanda suka yi gumurzu a lokacin yakin sun kasance kamar wani danba na kafa kasashen biyu. Sai dai kuma kasar Turkiyya ta musanta zarge-zargen da ka yi mata.

Yarima Charles na Ingila da autansa yarima Harry da sauran manyan baki daga fadin duniya sun halarci gangamin.