Ana sake zabe a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban hukumar zaben Najeriya, farfesa Attahiru Jega

A yau Asabar ne hukumar zaben Najeriya ke sake gudanar da zabe a wasu mazabu a jihohin Taraba da Imo da Abia domin kammala zaben gwamnoni jihohin.

A ranar 11 ga wannan watan ne dai aka gudanar da zabukan gwamnonin jihohi a fadin kasar, amma wasu matsaloli suka hana kammala na jihohin.

Rahotanni na cewa kawo yanzu hukumar ta INEC ta kammala shirye-shirye wajen ganin an gudanar da sahihin zabe a jihohin.

Haka kuma, an jibge jami'an tsaro a wurare da dama na jihohin domin bai wa mutane damar kada kuri'a cikin lumana.

Alamu dai na nuna cewa zaben kujerar gwamnan na jihar Taraba dai yana cike da tarihi.

Idan 'yar takarar jam'iyyar APC, Sanata Aisha Alhassan taci to za ta kasance mace ta farko gwamna a kasar.

Haka kuma idan dan takarar PDP, Ishaku Darius, ya samu nasara to jihar za ta kasance wadda jam'iyyar PDP ba ta taba faduwa zabe ba.