Jirgin kasa ya kashe mutane 14 a Macedonia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin kasa ya kade 'yan cirani 14 a Macedonia.

Jirgin kasa ya kashe a kalla mutane 14 lokacin da suka hau kan hanyarsa a kasar Macedonia.

Rahotanni da aka samu ya nuna cewa mutanen da suka mutu, suna cikin wata tawagar matafiya ne su 50, kuma yawancinsu sun fito ne daga Somalia da Afghanistan.

Lamarin ya faru ne a lokacin da suke tafiya a cikin dare a kan layin dogo.

Mutanen, wadanda 'yan cirani ne, suna tafe ne a wata sananniyar hanyar da ta bulle zuwa Balkans, hanyar da bakin haure ke bi domin tsallakawa zuwa Turai da kafa.