Sankarau ya hallaka mutane 129 a Nijar

Hakkin mallakar hoto Mike Goldwater World Vision
Image caption Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon cutar sankarau, ciki har da yara da mata

Cutar sankarau wacce ta barke a farko watan Janairu a jamhuriyar Nijar ta hallaka mutane 129.

Ministan lafiyar kasar Mano Aghali, wanda ya bayyana adadin ya ce kawo yanzu mutane 1,150 ne suka kamu da cutar.

Hukumomi a kasar sun kaddamar da aikin allurar riga-kafi a makarantu da ke fadin Yamai babban birnin kasar domin kawar da cutar.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Nijar ta sanar da rufe makarantu a Yamai a wani mataki na magance cutar.

A duk shekara a kan samu barkewar cutar sankarau a kasashe da dama da ke kudu da hamadar Sahara a nahiyar Afrika.