Shirin karasa zabe a Taraba, Imo da Abia

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Afrilu a ya bar baya da kura

Hukumar zaben Nigeria - INEC ta ce ta kamalla shirin karasa gudanar da zabe a wuraren da ba a kammala zabensu ba a jihohi uku na kasar.

Za a gudanar da zabukan ne a jihohin Taraba da Imo da kuma Abia.

Zabukan da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, za su bayar da damar tantance 'yan takarar da suka sami nasara a zaben gwamnoni da wasu kujerun majalisun dokoki na jihohin da abin ya shafa.

A jihar Taraba, INEC ta soke zabuka a wasu kananan hukumomi kuma sakamakon zaben da aka yi a ranar 11 ga watan Maris ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar PDP, Darius Ishaku da kuma Sanata Jumai Alhassan ta APC su ne ke kan gaba a wayan kuri'u idan aka kwatanta da sauran 'yan takarar.

Sai kuma jihar Imo, inda Rochas Okorocha na APC yake hamayya da Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP.

A jihar Abia kuwa, Dr Okezie Ikpeazu na jam'iyyar PDP ne ke ja-ni-in-jaka a kujerar gwamnan tsakaninsa da Alex Otti na jam'iyyar APGA.