An kashe mai fafutuka a Pakistan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu fafutukar kare hakkin dan adam a lardin Balochinstan su ma sun yi tofin alatsine da kisan

Frai ministan Pakistan Nawaz Sharif, ya jagoranci, yin Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wata fitacciyar mai fafutukar kare hakkin dan adam, Sabeen Mehmud.

Frai ministan ya kuma umarci 'yan sanda su gudanar da cikakken bincike kan kisan.

A ranar Juma'a da dare ne aka harbe matar, mai shekara 38, lokacin da take kan hanyarta ta komawa gida a Karachi, a mota, bayan ta gudanar da wani taron karawa juna sani.

Taron da ya kasance kan zargin hannun sojojin Pakistan a azabtarwa da kuma kisan masu fafutukar kare hakkin dan adam na kasar.