Saudi Arabia: An kama wanda ya hallaka 'yan sanda 2

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kungiyar IS ta ba wani umurni ya kai wa 'yan sandan Saudiyya hari.

Jami'an Saudiyya sun ce mutumin nan da ya harbe wasu 'yan sanda 2 har lahira a Riyadh babban birnin kasar, ya aikata hakan ne bisa umurni daga kungiyar IS ta Syria.

Mohammed Abdulrahman Abu Niyan, wanda dan asalin Saudiyya ne, ya shaida wa hukumomi cewa shi ya aikata kisan.

Ya kuma amsa laifin raunata wasu 'yan sanda guda 2 a makamancin wannan harin a cikin watan Maris.

Jami'an sun ce ya kai hare-haren ne bayan ya gana wani wakilin kungiyar IS da ke garin Riyadh a Saudiyya.